asirin wanda yake amfani da sunan jaruman kannywood a Facebook yayi lalata da yan mata ya tonu.

Asirin wani matashi wanda yake amfani da sunan Wasu daga cikin jaruman finafinan hausa na masana’antar kannywood yatonu, inda matashin bayan yashiga hannu yafito yayi bidiyo yana mai bada hakuri.
Matashin mai suna Abdullahi Sa’idu,ya bayyana cewa yana amfani da wani shafin mai dauke da sunan darakta Abubakar Bashir mai shadda,wanda akafi sani da king of box na masana’antar Kannywood.

Matashin ya bayyana yanda yakeyi har ya yaudari yan mata dasunan shine mai shadda, inda zasu fara tattaunawa da mace,sai ya dauki wata lambar tasa ta biyu ya tura mata yace taje suyi magana da yaronsa.
Bayan sun fara magana da ita a matsayin tana magana da yaronsa, sai ya nuna mata cewa shiga harkar fim ko kuma zama daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood ba wuya idan har zatabi ka’idoji da dokoki.
Daga nan sai ya nuna mata cewa idan har tanaso tashiga harkar fim dole sai ta dau zabi daya cikin biyu, na farko kodai ta bada kudi, na biyu ko kuma ta bashi kanta.
“Idan bayan munyi magana ta dau zabin cewa zata bani kudi,sai na tura mata account number taturo kudin.Idan kuma Ta dauki zabi nabiyu(tanason muyi lalata) sai nace ban yarda ba,nafi bukatar kudin“.inji Abdullahi Sa’idu.
Daga karshe dai matashin ya karyata kansa, kamar yanda zaku gani a bidiyon dake kasa 👇👇sannan kuma zaku ga asalin mutumin dake yaudarar mutane.
“yanzu dai inaso na gayawa jama’a cewa, ba Bashir mai shadda bane yake hira da mutane, ni Abdullahi Sa’idu, nine nake hira ina yaudarar mutane dasunan bashir mai shadda.
Ina mairokon dan allah dan annabi hukumar yansanda dakuma bashir mai shadda, dama sauran jaruman kannywood da duk wanda na yaudara su yafemin,insha allahu hakan bazata sake faruwa ba, ina mai bada hakuri,ayafemin” injishi.
Ga bidiyon nan akasa ku kalla kugani 👇👇👇
Idan zaku tuna ba tun yau ake samun irin wadannan mutane ba, ma’ana ake kama masu amfani da sunan Jaruman finafinan hausa na kannywood a kafafen sadarwa suna damfara dasu.
kwanakin baya ma anka ma wanda yayiwa maryam booth kazafi sannan aka hukuntashi.
Sababbin Hotunan jaruma maryam yahaya da nafisat abdullahi wadanda suka janyo musu cece-kuce.








