Kannywood

martanin Aminu s bono ga ladin chima ya hargitsa kannywood

Ladin chima: ana biyana 2000 a duk fitowa da na yi a film

Bayan wata tattaunawa da bbc hausa ta yi da wata tsohuwa mai suna ladin chima kan batun yadda ake biyanta a duk lokacin da ta yi wani role a kannywood, inda ta shaida wa bbchausa cewa ana biyanta dubu biyu zuwa biyar a duk wani film da ta ke fitowa, sannan kuma ba a taba biynta fiye da hakan ba, wannan batun ba karamin bacin rai ya jawo a zukatan mafi yawancin jaruman knnywood ba musamman ma manyan jarumai. A nan kuma mun kawo muku yadda martanin aminu s bono ga ladin chima ya hargitsa kannywood wanda ya jawo naziru sarkin waka da falalu a dorayi da ali nuhu su ka mai da martani.

Abinda ladin chima ya shaidawa bbc hausa

A yayin wata tattaunawa da bbc hausa ta yi da jaruma ladin chima a cikin shirin daga bakin mai ita, ta bayyanawa bbc cewa babban dalilinta na kasa mallakar gidan kanta ba komai ba ne face rashin biyanta da kirki da producers da kuma directors basa yi.

Ladin chima ta bayyana cewa mfi yawancin lokutan da ta ke fitowa afinafinai, ana biyanta tsakanin dubu biyu zuwa dubu biyar ne kawai wanda kuma tun da t far harkar fim bata taba samun wanda ya biyata sama da abinda ta ambata ba.

Jarumar ta koka d yadda sana,ar fim ta kasa siyamata gida ko da kuwa gidan kasa ne. ta ce hakan b karamin abun takaici ba ne ba a gareta. Sai dai kuma wnnan batu na ladin chima ba karamin mamaki ya ba mutane ba jin cewa har yau ko gidan kanta bata mallaka ba duk da ta dade ana damawa da ita a masanantar kannywood.

To amma kuma bayan jaruma ladi chima ta bayyana yadda wannan lamarin ya kasance mata, daga masana’antar kannywood an samu rarrabuwar kawuna, inda wasu ke Allah wadai da yadda aka ci amanar ta wasu kum su ka koka da yadda ta watsa musu kasa a ido duk da cewa sun yi iya kokarinsu a kanta. Bugu da kari wasu jarumai kamar Ali Nuhu da Falalu A Dorayi sun musanta batunta na cewa dubu biyu zuwa biyar ne ake biyanta, shi kuma a nasa bangaren Aminu S Bono  ya nuna damuwarsa matuka inda hakan har sai da ya jawo aka yi cece ku ce da shi a kafar sada zumunta ta tiktok, ga dai bidiyon ku kalla.

Abinda Aminu S Bono ya ce

Kamar yadda mu ka gani a cikin wannan bidiyon za mu ga yadda aminu s bono ya ambato cewa sun hada kudi sun amsawa ladin chima gidn haya wanda mai gidan daga baya ya ki amincewa da zamanta wai saboda shi gidansa sai amare ne kawai zai iya ba hayarsa.

Sai kuma daga bisani Bono ya kara cewa sun hada kudi sun siya mata gida wanda kuma ba iya shi s bonon ne kawai ya bayar da tallafi wajen siyen gidan ba, amma dai akwai mutane da yawa da su k bada gudun mowarsu. Saboda haka aminu s bono na ganin abinda ladin chima ta fada a matsayin wani kalami da bai dace  ce ta furta ba.

Har wa yu a tattaunawar da aka yi da aminu s bono, ba iya a batun ldin chima aka tsaya ba, domin kuwa tattaunawar ta hada da batun kallon da akewa yan kannywood a matsayin yan iska kuma masu lalata tarbiyya. A wannan bangaren s bono ya bayyana cewa ba iya yan kannywood ne kawai ake samun bara gurbi ba, hatta cikin sauran mutanen gari ma ana samu. Domin a cewarsa, wasu yan matan ma cikin shege su ke yi a gaban iyayensu abinda ba a taba samu ba a cikin yan matan kannywood ba.

Sannan kuma aminu s bono ya kara bada misali da yadda yan mata ke yin fitsara a tiktok wanda har rikici da zage-zage ake ganinsu su na yi, amma ba a taba ganin yan kannywood a cikin irin wannan tabarar ba. Saboda haka idan za a yi laakari da wannan kadai, ya isa ya zama misali na cewa tabarbarewar tarbiyya a kasar hausa bata da alaka da kannywood ta kusa ko ta nesa. Wannan shi ne kadan daga cikin raayin aminu s bono.

Abinda Ali Nuhu ya ce dangane da batun Ladin Chima

Ali nuhu ya kasance sarki a masana’antar kannywood, sannan kuma daya daga cikin wadanda su ke sanya ladin chima a cikin finafinan su. Domin kuwa ko a cikin sabon series film da ali nuhu ke yi a yanzu haka mai suna alaka akwai ta a ciki. Kenanko ta gaba ko ta baya babu yadda Ali nuhu zai iya fidda kansa a cikin zargi dangane da kalaman ladin chima.

A saboda haka ne jarumi Ali Nuhu ya fito ya mayar da martani ga wannan dattijuwar jarumar idna a cikin kalamansa ya bayyana cewa lallai shi kam a nasa bangaren yana biyanta hakkin aikinta saboda haka bai kamata ta yi kudin goro wajen hukunta dukkan masu sanyata a finafinai da kalma daya ba.

Ali Nuhu ya bayyana cewa ko a wannan film din nasa mai dogon zango mai suna alaka sai da ya biyata naira dubu arbain 40,000, kaga kenan ba adalci ba ne da ta ce wai babu mai biyanta sama da dubu biyar a film.

Martanin Falalu a Dorayi ga ladin chima

Shi ma Falalu a dorayi a nasa bangaren bai ja bakinsa ya yi shuru ba, domin kuwa sai da ya maidawa ladin cima martani dangane da kalamanta. Sanin kowa ne cewa falalu a dorayi shi ma producer ne sannan kuma babban director saboda haka idan har ana biyan ladin chima kudade masu tsoka to lallai shi ma zai sani.

Saboda haka ya bayyana cewa batunta kwata kwata ba haka ya ke ba, amma kuma sun yi mata uziri kuma basu yi mamakin jin abinda ta fada ba domin akwai rikicin tsufa a tare da ita. Falalu A Dorayi ya bayyana cewa tsakaninsa da ladin chima akwai fahimta da kuma girmamawa, domin kuwa har shawara na shiga a tsakaninsu.

Falalu A Dorayi ya bayyana cewa sau dayawa jaruma ladin chima tana kiransa ta fada masa idan wani wani ya mata alheri shi kuma ya kira ya yi godiya, sannan kuma du lokacin da ta yi masa aiki yana biyanta da kaso mafi tsoka domin tamkar uwa haka ya dauketa. Amma dai yadda ta yi musu jam’i ta basu hukunci iri daya bai masa dadi ba.

Karanta >>Yadda wani matashi ya kira hadiza gabon karuwa a bainar jama’a

 

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button