Labaran Duniya

Rundunar yan sandan jihar kano takama gagararren dan damfarar da aka dade ana nema ruwa a jallo mai suna ALJAN.

Rundunar yan sandan jihar kano tafitar da sanarwar kama gagararren barawo kuma dan damfara wanda ta dade tana nema ruwa a jallo mai suna,Sabitu ibrahim, wanda akafi sani da aljan da kuma karin wasu masu laifin tare dashi.

Sanarwar hakan tafito ranar asabar 27 gawatan November 2021 daga bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar kano, DSP Abdullahi haruna kiyawa,wanda ya bayyana cewa dama can an dade ana neman matashin domin akamashi sakamakon laifukan dayake aikatawa.

A lokacin da aka kama matashin wanda yake zaune a unguwar kaburma, ankamashi da mashin mai kafa uku(adaidaita sahu) wanda ya tabbatar wa da yan sanda cewa babur din satoshi sukayi shi da abokin aikin nashi.

Sannan kuma bayan shi ankama wasu masu siyen kayan sata wadanda ake kawowa baburan sata suna siya(barayin zaune) duka acikin masu laifin.

Ga cikakken videon su nan akasa kudanna domin ku kalla.

https://www.youtube.com/embed/uh7H04mNR1s

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button