Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un : Dalibar BUK ta rasu tana tsaka da sallah a dakin kwanan dalibai.
Wata daliba dake a ajin karshe (400 level) a tsangayar ilimi ta jami’ar bayero dake kano (BUK),Binta isah,tarasu tana ysaka da sallah a dakin kwanan dalibai a ranar juma’a 26/11/2021.
Dalibar wacce tafito daga jihar kogi, tarasu misalin karfe 7:00 na dare bayan tasha fama da yar gajeruwar rashin lafiya, wacce ake zargin cewa ciwon kirjine.
DAILY NEWS HAUSA ta wallafa cewa, daraktan lafiya na jami’ar ya tabbatar da faruwar al’amarin, yace binta taje asibitin new campus dake jami’ar a ranar 24 ga watan November,tayi korafi cewa tana fama da ciwan kirji.
Yakara dacewa jami’an dasuka duba mamaciyar sun bata magani sannan suka zayyana mata yanda zata rinka amfani dasu.
Darakatan yace daga nan binta tasamu sauki, domin ta cigaba da halartar lakca ranar alhamis da juma’a, kuma tacigaba da ayyukan karatunta.
A halin yanzu jami’ar tasanar da dan’uwan dalibar, wanda yake zaune acikin garin kano, game da faruwar al’amarin, sannan kuma shugabannin jami’ar sun jajantawa ahlin mamaciyar.








