Labaran Duniya

Duniya ina zaki damu : Wani matashi yayiwa dan’uwansa yankan rago.

Wani matashi da aka bayyana sunansa da junaidu ahmadu yaro, mazaunin karamar hukumar katsina ala dake jihar benue, ya cakawa dan’uwansa wuka a sanadin fadan cultism a wani otal.

Bayan ya aikata laifin kisan yayi yunkurin guduwa sai jami’an yan sanda suka kamashi a rice mill house quarters dake karamar hukumar katsina ala cikim jihar benue.

Marigayin da aka kashe mai suna, Nurain dan bala, yataso ne daga jihar calabar zuwa katsina ala domin halartar bikin murnar zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta, annabi muhammad s a w.

Jaridar DAILY NEWS HAUSA ta ruwaito cewa ahi marigayin da aka kashe, Ya sauka a keke napep kenan junaidu ya daba masa wuka, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.

Zuwa yanzu dai matashin yana ofishin yan sanda yana amsa tambayoyi, a halin da ake ciki ya lissafo mutane kimanin goma wadanda aka aikata fadan dasu,dukkansu yan sanda sun bisu sun kamasu.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button