Shin da gaskene minista fantami ya hadu da jaruma hadiza gabon a ofis dinsa.
Al’umma da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu akan wani hoto da yake ta yawo adandalin sada zumunta musamman ma na facebook da whatsapp.
Hoton ya na dauke da jarumar fina-finan hausa, hadiza Gabon, da kuma ministan sadarwa,Ali isah fantami, a tsaye a ofis dinsa shida jarumar, har ma jikinsu yana manne da juna.
KARANTA : GIDAN BADAMASI SEASON 4 : Anfara daukar Shirin gidan badamasi season 4, ga kadan daga ciki.

Sai dai kuma daya daga cikin masu yawan rubutu a dandalin sada zumunta na Facebook, musamman ma akan malaman izala da kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari, DATTI ASSALFIY, yayi karin haske akan hoton da ake yayadawa.
A wani rubutu dayayi ya bayyana cewa “Hoton da ake yadawa wai minista fantami yahadu da hadiza gabon ba gaskiya bane”.
KARANTA : VIDEO : MUSABBABI HAUSA FILM DAGA KAMFANIN DORAYI FILM PRODUCTION.
Yakara dacewa ” Hoton anyi editing ne aka hada akan application,malam bai taba haduwa da hadiza gabon ba, kuma bai taba kulla soyayya da hadiza gabon ba, layin jirgi daban na mota daban”
“Jama’a duk inda kukaga wannan hoton ba gaskiya bane, sharri aka tsara domin a bata masa suna.
Ya karkare rubutunsa da ” muna fatan allah ya tsare mana rayuwar malam da mutuncinsa, allah ya shiryar da masu yimasa batanci”.
Daga karshe bayan bunciken da mukayi mun gano cewa wannan hoton karyane, kuma hadine wani yayi domin batawa malam suna.

Ga dai asalin hotonnan kafin a canzasa, nasama shine asalin hoton,sai kuma wasu bata gari sukayi amfani da shi suka kirkiri na kasan.









One Comment