Jaruma Rahma MK, Matar Gwamna A shirin kwana chasa’in tayi auren sirri.
Matar bawa mai kada acikin shirin kwana casa’in, rahama mk,tayi auren sirri ayayin da ake tsaka da shirya fim din.
A rahoton da DIMOKURADIYYA ta fitar ya bayyana cewa a ranar asabar 6 ga watan November aka daura auren jarumar da angonta a gidansu dake cikin garin kano acikin sirri yanda ba kowane yasani ba.
Acewar jaridar, dama dai jarumar ta dade tanason tayi aure amma hakan bai samu ba sai yanzu.
- Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko
- Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai
Gidan jaridar sun tuntubi jarumar ta wayar tarho inda itakuma jarumar ta tabbatar da maganar sannan ta kara dacewa.
“Kamar yanda nafada maka kwanaki 3 dasuka gabata, zanyi aure a wannan ranar insha allahu, to gashi allah yakawomu kuma andaura auren, ina fatanna haihu kuma na mutu a dakin mijina”. In jita.
Sannan jarumar tace zata cigaba da fitowa a cikin shirin kwana casa’in, sai dai kuma sauran fina-finan ne babu tabbas akan cigaba da fitowa acikinsu.








