siyasa

Saura kadan na fasa kwai kowa yasan abunda yake faruwa-muhuyi magaji

Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano, Barista muhuyi magaji rimin gado, ya bayyana cewa nan bada jimawa zai fasa kwai.

Barista muhuyi magaji ya bayyana hakanne a wata hira da gidan redion FREEDOM RADIO sukayi dashi.

Ya bayyana cewa takun sakar dayasa akacireshi daga shugabanci bai wuce saboda kin amincewa a yi almundahanar wasu kudade ba.

“Lokacin da aka dakatar dani daga hukumar bawani kudi gareni ba, du-du-du basu wuce dubu 73000 ba”.

Yacigaba da cewa “ni bana tsoron bincike yabiyo takaina, domin kuwa babu wani abu danake tsoro a bangaren binciken nan saboda inada tarin shaidu dakuma hujjoji wanda zasu kareni akan zargin da ake min”.

Yakara dacewa”badan ace inada abubuwan da zasu zamar min shaida ba, dako wannan hirar ban isa nazo nayi daku FREEDOM RADIO ba, kuma tuhuma ta da akace anayi wannan kawai taba mutuncina akeyi, domin kusan kowa damuke tare yasan ina zuwa ganin likita”.

Idan zaku tuna a watannin baya ne gwamnatin jihar kano ta sauke muhuyi magaji daga mukaminsa bisa zarge-zarge da dama a lokacin da yana shugaban hukumar.

Sai dai kuma bayan nan yan sanda sun gayyaceshi dayazo ya masa wasu tambayoyi a ofishin yan sandan.

Daga baya hukumad yansan dan ta wankeshi tareda bashi fasfo wanda hakan ke nufin babu wani zargi akansa.

Sai dai kuma wannan baiyiwa gwamnan kano abdullahi ganduje dadi ba, inda yanzu haka Ganduje yake shirye-shiryen kama muhuyi magani rimin gado a karo na biyu.

KARIN WASU LABARAN

  • “Kwankwasiyya ce muke” sabuwar wakar kosan waka mai zafi.

    Shahararren mawakin kwankwasiyya, wanda yake jihar katsina, kosan waka, yasaki sabuwar wakar jagoran tafiyar siyasar kwankwasiyya na duniya, engr dr rabi’u musa kwankwaso.

    Tun a kwanakin baya mawakin yayi magana akan sakin sabuwar wakar tasa wacce tazo da sabon salo.

    Ga videon wakar nan akasa ku more kallo kyauta.

    Sabuwar wakar kosan waka “kwankwasiyya ce muke”

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button