siyasa

Yan kasuwar kwari sun kai karar ganduje gurin allah a wani taron alkunuti dasuka gabatar.

A yau talata 12 ga watan October na shekarar 2021, yan kasuwar kantin kwari sukayi gangami suka taru suka kai karar gwamnan kano abdullahi ganduje gurin allah sakamakon zarginsa da gine rumfunansu na kasuwanci.

A wani bidiyo da jaridar Daily Nigerian hausa ta wallafa, ya nuno jama’a da dama bila adadin suna ta addu’a dakuma kai kokensu ga ubagiji bisa wannan masifa data fado musu.

Wanda yake daukar bidiyon yabayyana cewa, gurin hanya ce ta bayin allah dakuma sarari wanda al’ummar annabi suke samun na abinci, amma ba fili bane da za’ace na gwamnati ne ba.

Ga dai videon nan ku kalla kuga yanda abubuwan suka gudana 👇👇👇

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button