Kannywood

Wani matashi ya kira Hadiza gabon karuwa a bainar jama’a

Wani matashi ya kira Hadiza gabon karuwa a bainar jama’a

A yayin da masana’antar kannywood ke kokarin ganin ta kyautata yadda ta ke gudana da shirye-shiryen finafinai domin ganin an samu dacewa da juna tsakanin finafinan nasu da kuma tsarin addini da kuma al’ada a kasar Hausa, a daidai lokacin ne kuma wasu daga cikin jaruman ta ke fuskantar tsangwama da matsin lamba a cikin al’umma a bisa zargi.

A nan ma daya daga cikin jaruman ta ne ke fuskantar tuhume-tuhume daga mabiyan masana’antar. Hadiza Aliyu gabon dai ta samu sako daga wani matashi da ya fito a fili ya kirata da karuwa. 

Matashin mai suna Ahmad Babayo ya bayyana cewa Hadiza gabon ce ta fara tura masa sakon neman kulla Abuja(friend request) shi kuma ya amsheta, wanda daga bisani kuma ya ce ya ga rubutun da ta yi na shekara neman mijin aure.

Matashin ya ci gaba da cewa, hakika Hadiza Aliyu gabon bata dace da tsaran matan da zai iya aura a, domin kafin a fara saka su a Film sai an yi ta yi musu lalata.

Haka kuma ya cigaba da cewa, dukkan matan kannywood ana yin lalata da su, saboda haka Hadiza gabon ma an shi yi mata lalata. Matashin ya ce dukkan mutumin kirki ba zai so ace ya auri karuwa ba, domin kuwa idan Æ´aÆ´ansu suka taso za dinga cewa uwarsa karuwa wanda hakan zai iya taba kimarsu.

Daga karshe Ahmad Babayo ya yi kira ga Hadiza Aliyu gabon da ta fadawa sauran abokan aikinta na masana’antar kannywood cewa ga irin cin mutuncin da ya yi mata saboda haka idan da mai iya daukar wani mataki sai ya yi.

Karanta>>https://hausanovels.org/tohfa-yan-hisbah-sun-kama-fati-washa-a-gidan-gala-na-jihar-jigawa/

Martanin da Hadiza gabon ta yiwa wanda ya kirata da karuwa

Bayan jaruma Hadiza Aliyu gabon ta karanta sakon rashin mutuncin da Ahmad Babayo ya turo mata, sai ta garzaya zuwa shafin ta na twitter ta sanya screenshot na hoton sakon da aka turo mata, sannan kuma ta yi martani cikin layi 1 wanda ya matuÆ™ar ja hankalin al’umma.

A cikin martani nata ta roki Ubangijin ya bashi  zaman lafiya da Soyayya a rayuwarsa.

Wani matashi ya kira Hadiza gabon karuwa a bainar jama'a

Hakikanin gaskiya wannan martanin da Hadiza gabon ta yiwa wannan bawan Allah ba karamin mamaki da kuma burge mutane ya yi ba, a yayin da aka saba ganin yadda yan kannywood ke yiwa masu yi musu irin wannan sakon zazzafan raddi mai cike da rashin mutunci.

Za ku iya kallon wannan bidiyon domin jin cikakken rahoton.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button