siyasa

APC :ZABEN ABDULLAHI ABBAS YA JANYOWA JAMI’IN DAN SANDA ALAKAKAI HAR TAKAI GA BINCIKE.

Wani jami’in dan sanda da aka bayyana sunansa da Bashir muhammad ya fada tsaka mai wuya, sakamakon hango sa da’akayi acikin hoto yana kada kuri’a a zaben da aka gudanar ranar asabar data gabata a dakin taro na sani abacha stadium.

Jami’in yafada komar bincike daga Mataimakin Babban sifetan yan sanda na kasa shiyya ta daya dake kano,inda rundunar yan sanda tace zatayi bincike akan jami’in nasu wanda yake jami’in kula da abdullahi abbas ne.

Mai magana da yawun shiyyar, DSP Abubakar zayyanu ambursa ya bayyana cewa, idan har ansameshi da laifi to babu shakka za’a hukuntashi,domin tuni aka tura lamarin zuwa sashin binciken shiyyar.

Mutane da dama dai suna ta bayyana ra’ayinsu akan wannan maganar,domin zaben jam’iyya abune wanda yashafi delegate da jam’iya, bawai jami’an tsaro ba.

Read Also

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button