Yanzu-yanzu: uwar jam’iyar Apc ta kasa tayi watsi da zabensu malam shekarau ta dau abdullahi abas.
uwar jam’iyar APC ta kasa tayi watsi da zaben da tsaginsu malam ibrahim shekarau sukayi a kano inda ta yarda da abdullahi abbas a matsayin halastaccen shugaban jam’iyar APC reshen jihar kano.
Sanarwar tafito daga daraktan yada labaran jam’iyar na kasa,alhaji salisu na’inna dambatta ne ya bayyanawa freedom radio haka.
“Yanda Tsarin jam’iyar yake shine,duk inda gwamna yake to shine jagoran jam’iyar” inji shi kamar yanda Freedom radio ta wallafa.
“Saboda haka duk wadanda sukayi zabe sabanin wannan to wannan zaben ba halastacce bane”
A wani rahoto daya fitar a ranar 17 ga watan October 2021, salisu yahaya hotoro, daya daga cikin yan jarida kuma wanda ya halarci gurin zaben da aka gabatar a jiya 16 gawatan October, yabayyana a shafinsa na Facebook cewa labarin ya tabbata.
Zaben wanda aka gudanar ajiya yabar baya da kura, inda tsagin gwamnatin kano sukayi zabensu daban, yayinda suma tsagin tsohon gwamnan jihar kano sanata ibrahim shekarau sukayi nasu daban.



