Yanzu-yanzu: Ganduje yasauke mu’az magaji dan sarauniya daga mukaminsa a karo na biyu.
Gwamnan jihar kano, dr abdullahi umar ganduje, yatsige muaz magaji daga mukaminsa na shugaban kwamitin kula da aikin janyo bututun iskar gas na AKK saboda rashin tabuka abun kirki dakuma zagon kasa.
Bayanin hakan yafito daga cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar kano, malam muhammad garba yafitar a daren litinin.
Wannan ne karona bigu da gwamnan kano abdullahi ganduje ya tsige muaz magaji wanda akafi sani da dan sarauniya daga mukaminsa.
A baya gwamnan yasauke shi daga mukamin kwamishinan ayyuka na jihar kano,sakamakon wani post dayayi a shafinsa na dandalin sada zumunta wanda yake nuni dacewa yayi murna da rasuwar marigayi Abba kyari.
- Dalilin da yasa amare basa cin kazar da ango ke kawowa a daren farko
- Wani kare ya mutu har lahira bayan ya shinshini dan kampai
Sai dai kuma muaz magaji yayi magana akan wannan tsige shin da gwamnan kano yayi daga mukaminsa.
Daga cikin maganganunsa akwai inda yake rantsuwa da allah cewa, tun can da yaso yabar aikin amma kuma saboda bayaso ace yayiwa gwamna ganduje butulci shiyasa yazauna.
Wasu da dama suna ganin cewa wannan maganar kamar akwai siyasa acikinta.
Inda wasu suke ganin kamar yawan maganar muaz magaji dan sarauniya ita tajamasa wannan korar kare da akayi masa.


