Yan sanda sun cafke mutumin dayayiwa yara kanana guda 4 fyade yan kasa da shekara 7 a jihar borno.
Rundunar yan sandan jihar borno tayi nasarar cafke wani mutum mai suna abubakar baba da laifin yiwa yara kanana guda hudu fyade.
Kungiyar RIGAR YANCI INTERNATIONAL ta ruwaito cewa,mutumin da ba’abayyana shekarunsa ba, an bayyana cewa yaran dayayiwa fyaden sun hada da yan shekaru hudu guda 2 sai yar shekara 6 dakuma yar shekara 7.
Wanda aka kama da laifin yana daya daga cikin mutum 58 da rundunar yan sandan jihar borno ta kama bisa aikata laifuka daban-daban, kama daga laifin fyade, safarar miyagun kwayoyi dakuma kamasu da aiki da kungiyar asiri.anyi wannan kamene acikin watanni hudu dasuka gabata acikin birnin babban birnin maiduguri, majalissar bama dakuma hawul na nijar.
KARANTA : Duniya ina zaki damu : An kama wasu yan biyu maza bisa zargin yiwa yarinya yar shekara 9 fyade.
Da yake gabatar da wadanda ake zargi ga manema labarai, kwamishinan yan sandan jihar borno, Abdu umar, ya bayyana cewa “a ranar 23 ga watan oktoba an kama wani mai suna, Bilyaminu saleh, mazaunin gwange bisa kamashi da laifin yaudarar yarinya mai shekaru 6 yajata masallaci, inda anan yayi matawa wannan aika-aika ta karfin tsiya”
“Bayan haka, a ranar 4 gawatan November shima abubakar baba n kwange aka kamashi bisa laifin yaudarar yan mata (masu karancin shekaru daga 7 zuwa kasa) yayi lalata dasu ta karfin tsiya.
Kwamishinan ya kara dacewa ankama masu laifi dayawa wadanda suka hada da Abubakar muhammed wanda shekarunsa basu wuce 17 ba, ana zarginsa da korar wata bafulatana ta hanyar yi mata fyade.
Sannan kuma ga Mohammed isah da umar mohammed, inda suka hadu da wata saratu goni a gabar kogi, inda sukayi mata fyade da karfin tsiya.
Ya karkare da cewa da zarar an kammala bincike za’a tura wadanda ake zargi zuwa kotu domin yanke musu hukunci




