Friday, 03 December, 2021

Daga karshe Wanda yayiwa maryam booth kazafi akan andena sata a film yazo hannu.


A kwanakin baya wani labari ya dinga yawo a kafafen sadarwa musamman na Facebook a game da rashin ganin jaruma maryam booth acikin fina-finan hausa kwanan nan.

Labarin wanda ya bayyana cewa maryam booth tace, tun daga lokacin da akaga bidiyon ta tsirara daraktoci suka dena sakata a film kuma aka dena ganin mutuncinta a cikin al’umma.

Sai dai kuma a jiya laraba maryam booth ta wallafa wani bidiyo mai dauke da wani matashi yana magana, acikin batun matashin ya tabbatarwa da duniya cewa, wannan maganar da akai ta yadawa a kafafen sadarwa na cewa maryam booth tace andai na sanyata a film ba gaskiya bane, labarin karyane kuma shiya kirkireshi.

Matashin ya bawa jaruma maryambooth hakuri, inda yake cewa sharrin shaidanne kuma insha allahu hakan bazata sake faruwa ba.

A karkashin videon jaruman jaruma maryambooth tayi rubutu kamar haka.

Daga karshe dai jarumar ta gargadi mutane musamman ma bloggers dakuma YouTubers akan yada labaran karya, inda tace bazata cigaba da tsayawa ana bata mata suna ba saboda haka duk wanda yakara zata dau mummunan mataki akai.

0 comments on “Daga karshe Wanda yayiwa maryam booth kazafi akan andena sata a film yazo hannu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *